Akalla ministoci takwas ne aka gayyata wadanda suka yi aiki a karkashin tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari kan zargin cin hanci da rashawa, kamar yadda majiyar hukumar yaki da cin hanci da rashawa (EFCC) ta bayyana.Wasikun gayyatan dai, an bayyana cewa, sun bukaci tsofaffin manyan jami’an gwamnatin da su zo su yi bayanin yadda suka kashe kudaden da aka ware wa ma’aikatun su a wasu ayyukan da aka ware a lokacin da suka rike mukamansu.
An tattaro wasikun ne zuwa ga tsoffin ministocin kafin a dakatar da Abdulrasheed Bawa a matsayin shugaban hukumar.
Hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta fara gudanar da bincike a cewar majiyoyin hukumar.
Majiyar ta ce baya ga tsohuwar ministar harkokin mata, Pauline Tallen, wadda aka gayyace ta a makon da ya gabata bisa zargin almundahanar Naira biliyan 2 da kuma “bangaren kudaden da ake zargin an karkatar da su daga aikin wanzar da zaman lafiya na uwargidan shugaban kasar Afrika,” an kuma gayyaci wasu kusan bakwai.
Idan dai ba a manta ba a watan da ya gabata ne hukumar ta kama Sale Mamman, wanda kuma tsohon ministan wutar lantarki ne a zamanin mulkin tsohon shugaban kasa Buhari, tare da tsare shi bisa zargin almundahanar Naira biliyan 22 da ya shafi ayyukan wutar lantarki.
Hakazalika, an tattaro cewa tsohon ministan harkokin ‘yan sanda, Muhammad Maigari Dingyadi, shi ma an gayyaci shi kan yadda ake tafiyar da asusun ‘yan sanda.
Da yake magana game da batun sakaya sunansa, majiyar ta ce Dingyadi zai bayar da amsa kan zargin sayan motocin da aka gyara ga ‘yan sandan Najeriya a matsayin sababbi.
“To, ni ban san da wasikar ba, ban gani ba, watakila sun aika ofishin ne, zan yi tambaya daga ofishin,” in ji ministan harkokin ‘yan sanda, Dingyadi, ya shaida wa daya daga cikin wakilanmu kan lamarin. waya.