Gwamnan Kano Injiniya Abba Kabir ya kaddamar da tallafin aiki ga masu lalurar zuciya a Asibitin Malam Aminu Kano, wanda Kasar Saudiyya karkashin kungiyar Musulinci ta world league da kuma kungiyar taimakon Alumma a kasar saudi arabiyya suka shirya.
Farfesa Abdurrahman Abba Sheshe shine shugaban wannan asibitin Mal. Aminu Kano ya nuna farin cikin sa bisa wannan aiki da wannan gidauniya ta Saudiya ta kawo kano wanda kimanin mutum ashirin zasu amfana da aiki.