Gwamnan Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf ya amince da biyan kudin NECO ga daliban makarantun gwamnati 55,000.
Injiniya Abba Kabir Yusuf ya bukaci daliban da suka amfana da su yi aiki tukuru don ganin sun samu sakamako mai kyau.
A cewar Gwamnan, “A matsayina na gwamnatin da abin ya shafa, ya zama tilas mu tabbatar da cewa baku daina neman ilimi ba, kuma nan take na amince da biyan kudin jarabawar ga dalibai 55,000 a fadin jihar nan.
Ya kamata ku yi iya kokarinku kuma ku jajirce domin ku fito da kyakkyawan sakamakon jarrabawar da za ku iya farantawa jihar da iyalanku da kuma alfahari da ku.” Inji Gwamnan.
Ya kuma tabbatar wa al’ummar Kano cewa gwamnatinsa na fito da manufofi da tsare-tsare na inganta harkar ilimi, domin ilimi shi ne ginshikin ci gaban kowace al’umma.