Bayan shafe makwanni ana cece-kuce dangane da lafiyar Oluwarotimi Akeredolu, gwamnan jihar Ondo, da kuma tsawaita zamansa a jihar, ya mika mulki a hukumance ga mataimakinsa, Lucky Aiyedatiwa, a ranar Litinin.
Akeredolu ya rubuta wasika zuwa ga Olamide Oladiji, kakakin majalisar dokokin jihar Ondo, inda ya sanar da majalisar cewa Aiyedatiwa zai yi aiki a matsayin gwamna yayin da yake hutun jinya a kasar waje.
Halin da Gwamnan yake ciki ya haifar da fargaba a jihar, inda jam’iyyun adawa suka yi ta kiraye-kirayen ya mika mulki ga mataimakin gwamnan domin kaucewa rikicin tsarin mulki.
Shugaban majalisar ya tabbatar da cewa Akeredolu zai tafi hutun kwanaki 21 a kasar waje, daga ranar 7 ga watan Yuni zuwa 6 ga Yuli, 2023.Wasikar ta bayyana cewa an tsawaita hutun da aka fara daga ranar 7 ga watan Yuni zuwa 6 ga watan Yuli, 2023, saboda hutun da jama’a suka yi a ranar 12 ga watan Yuni (Ranar Dimokuradiyya) da kuma Eid el Kabir (28 da 29 ga Yuni, 2023).
Shugaban majalisar ya bayyana gwamnan a matsayin mai son zaman lafiya kuma mai son bin doka da oda.
Ya kuma yi masa fatan samun lafiya cikin gaggawa da hutu mai dadi tare da tabbatar wa al’ummar Jihar Ondo cewa Mataimakin Gwamnan zai tafiyar da al’amuran Jihar yadda ya kamata idan Gwamnan ba ya nan.