Sakataren yada labarai na gwamnan kano Hon Sanusi Bature Dawakin Tofa ne ya wallafa labarin inda yace
Gwamnatin jihar Kano ta rushe shataletalen gidan a daren jiya domin bukatun alumma.
Kafin rushe shataletalen, sai da gwamnati ta nemi shawarar injiniyoyi da kwararraru a harkar gini wadanda suka tabbatar cewa ginin shataletalen ba Shi da inganci kuma zai iya rushewa daga nan zuwa shekarar badi ta 2024.
Masanan sun bayyana cewa anyi amfani da soson katifa da kuma kasa maimakon amfani da kankare yadda aka saba
Haka kuma ginin ya yi tsawo a gaban gidan gwamnati Wanda ya boye fuskar Kofar Shiga gidan kuma yana hana jamian hango masu yin zirga-zirga-zirga-
Bugu da kari, shataletalen na haifar da kalubale ga zirga-zirgar ababen hawa saboda da girmansa wadda hakan na kare direbobi daga samun saukin yin amfani da hanyoyin da shataletalen ya hada.
Gwamnati na son a fahimci cewa daukar matakin rushe shataletalen ya zama wajibi domin sake gina wani cikin hanzari don samun ganin Kofar Shiga gidan gwamnati yadda ya kamata da kuma kiyaye lafiyar masu ababan hawa.
Sa hannu
Sanusi Bature Dawakin Tofa
Sakataren Yada Labarai na Gwamnan Jihar Kano
14 ga Yuni, 2023