Mutanen da jirgin kamfanin Tarco ya ɗebo sun sauka a filin jirgin sama na Nnamdi Azikiwe da ke Abuja da misalin ƙarfe 4:56 na yammacin jiya Asabar.
Hukumar agajin gaggawa ta Najeriya, NEMA, ita ce ta jagoranci ɗebo mutanen tare da haɗin gwiwar ma'aikatun harkokin waje da ta 'yan Najeriya mazauna ƙetare, da sauransu.
Sai dai har yanzu akwai ɗaruruwan 'yan Najeriyar da ke roƙon a kwashe su daga Sudan ɗin amma babu tabbas ko gwamnatin ƙasar za ta ci gaba da aikin kwashe su a yanzu.