Gwamnan jihar Zamfara Dauda Lawan Dare ya ce tun da aka rantsar da shi har zuwa wannan lokaci a cikin bashi yake mulki, saboda gadar mulki ba tare da kudi ba a asusun gwamnati.
Gwamnan Lawan a wata tattaunawa ta musamman da BBC, ya yi bayani a kan yadda ya tarar da gwamnati bayan ya sha rantsuwar kama aiki a ranar 29 ga watan Mayu har zuwa wannan lokaci.
Ya ce babu wani abin da gwamnatinsa ta tarar a cikin lalitar Zamfara, sai naira miliyan uku kacal.
"Kusan asusu guda na gani, watakila ince akwai kamar naira miliyan uku ko hudu ne a ciki", in ji Dauda.
Ya ce a halin yanzu yana bige-bigen neman rance domin samun kuÉ—in biyan ma'aikata albashi watanni hudu da suke bin gwamnati.Gwamnan Dauda da ke fayyace dalilan da suka sanya suke binciken tsohon gwamnan da nazartar yadda abubuwa suke a Zamfara ya ce a halin yanzu babu wuta a ma'aikatun gwamnati saboda ana binsu bashi na miliyoyin naira.
Sannan suma jami'an tsaro an daina biyansu kuÉ—aÉ—en alawus-alawus wata da watanni, harkar ilimi ya durkushe baki-daya.
"Yau da mu ke maganar nan duk wani dalibi na jihar Zamfara, bai rubuta jarabawar NECO da WAEC ba, saboda ana bin gwamnati kuÉ—i fiye da naira biliyan É—aya". Gwamnan Dauda da ke karyata ikirarin gwamnati da ya gada ta APC da ta ce ta bar rarar naira biliyan 20 da wasu daloli a cikin asusu, ya ce a halin yanzu ya soma cin bashi domin wasu ayyukan.
"Ina son a zo a nuna mana shin a wani asusu ne aka ajiye wannan kudi, kuma a nuna ma duniya shaidar cewa ga naira biliyan ashirin, É—omin na tabbatar ina samu wannan kuÉ—i zan biya ma'aikata kudinsu na wata hudu da ba a biyasu ba".
Sannan gwamnan ya ce da ake akwai wadannan kuÉ—aÉ—e a zahiri da tuni ya yi amfani dasu don taimaka wa jami'an tsaro a aikin da suke yi domin tabbatar da tsaro a cikin jihar.
"Yanzu haka sai da gwamnantinsa ta ciyo bashi domin magance matsalar rashin ruwan sha da ta addabi Zamfara".
Gwamna Dauda ya ce jihar ta shafe wata hudu babu ruwan sha ko da ya ke ya ce kawo yanzu matsalar tana nan amma gwamnatinsa ta fara aikin shawo kanta.
Gwamnan ya kuma yi alkawarin biyan ma'aikatan gwamnati albashi kafin babbar sallah.
Ya ce yanzu ya fito yana bige-bigen neman rance domi samun kuÉ—in biyan ma'aikatan ko rage wani É“angare na bashi9n watanni hudu da suke bin gwamnati.
Duk yadda zan bi na biya albashi idan Allah ya yada zan biyasu, domin na tabbatar cewa wannan hakki nasu na sauke musu, in ji shi Dauda.Tun hawan Dauda mulki ake samun takaddama tsakaninsa da tsohon gwamna da ya gada Bello Matawalle, abin da ya kai ga gwamnati ta gargadi tsohon gwamnan ya dawo da kadarorin gwamnatin da ke hannunsa.
Sannan gwamnatin Zamfara na ta fitar da sanarwa kan wasu zarge-zarge da take yiwa gwamnan da ya sauka.
Sai dai Bello Matawalle da mukarabansa sun sha fitowa suna musanta wasu zarge-zarge da ikirarin barin makudan kudaden a lalitar gwamnati kafin sauka.
Amma kafin wannan lokaci kwanaki Bello Matawalle ya bar mulkin an samu wasu rahotanni daga EFCC da ke zargin gwamnan da zargin karkatar da N70bn da bayar da kwangiloli ba bisa ƙa'ida ba.
"Kuɗin wanda aka samu a matsayin bashi daga wani banki domin aiwatar da ayyuka a sassan ƙananan hukumomin jihar, ana zargin gwamnan ya karkatar da shi ne," kamar yadda sanarwar EFCC ta bayyana.
Sannan sanarwar ta ce binciken hukumar ya nuna fiye da kamfanoni 100 ne suka karɓi wani kashi na kuɗaɗen ba tare da wata hujja da ta nuna an aiwatar da ayyukan ba a Zamafara
EFCC ta ce wasu daga cikin ƴan kwangilolin an gayyace su inda aka yi musu tambayoyi kuma sun yi zargin cewa gwamnan ne ya tilasta musu mayar masa da kuɗaɗen da suka karɓa daga asusun gwamnati ta hannun masu taimaka masa bayan da suka canja kuɗaɗen zuwa dala.
BBC