Gwamnatin Kano tace, har yanzu ba a yanke shawara kan matsayin sabbin masarautun da tsohuwar gwamnatin ta kafa ba.
jita-jitar da ake yadawa a shafukan sada zumunta, na gwamnatin jihar Kano ba ta dau wani mataki kan sabbin masarautun kamar yadda ake hasashe.
Cikin wata sanarwa da Sakataren Yada Labaran Gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar yace, Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusif, ya mika bukatar nada masu ba da shawara na musamman guda 20 wanda majalisar dokokin jihar ta amince da su a zamanta na yau.
Ana sa ran za a aika da jerin sunayen kwamishinonin da za su yi aiki a mako mai zuwa domin tantancewa.
Hakan nazuwa bayan da gwamnatin kanon ta rushe shatetalen shiga gidan gwamnatin wanda wasu suke gannin anruguje algaitar da akayi addo da ita ajikin shatetalen