Ya ce hakan ya faru ne saboda luwaɗi "laifi ne a idon dokar Kamaru.
Jakadan Faransa mai kula da ‘yancin ‘yan luwaɗi da maɗigo, Jean-Marc Berthon, ya so kai ziyara Kamaru ne daga ranar 27 ga watan Yuni zuwa 1 ga watan Yuli domin tattaunawa da hukumomi kan kare ‘yancin masu neman jinsi ɗaya.
Ziyarar da Mista Berthon ya so kai wa ta zo ne a daidai lokacin da hukumar sadarwa ta Kamaru ta gargaɗi kafafen yada labarai a kan tallata harkokin da shafi 'yan luwaɗi da maɗigo.
Ana taƙaita 'yancin ƴan luwaɗi da maɗigo a yawancin ƙasashen Afirka, wasu ƙasashe na suna tsaurara dokoki kan rukunin al'ummar.
A shekara ta 2021, ƙungiyar kare haƙƙin ɗan'adam ta yi tir da tsangwamar da ake yi wa ƴan luwaɗi da maɗigo a Kamaru.