Abdulqadir Dahiru, a wata sanarwa da ya fitar a Legas, ya ce hukumar ba ta da alaka da adireshin gidan jaridar ta yanar gizon: www.recruitmentfile.net da wasu ‘yan damfara suka samar.
“jaridar ta bayyana cewa wadanda suka cancanta su aika buƙatar neman aikin adireshin yanar gizon hukumar.
“An yi kira ga jama’a da su lura cewa wannan labari karya ne kuma babu wani daukar aiki da mu ke yi.
“A halin yanzu dai hukumar ta kai rahoton shafin yanar gizon ga hukumomin da su ka dace domin daukar matakin da ya dace,” in ji shi.
Dahiru ya ce duk sahihin bayanai game da ayyukan hukumar ana iya samun su a adireshin yanar gizon ta: www.pencom.gov.ng da kuma hanyoyin sadarwar ta: Facebook: @PenCom.gov, da Twitter: @PenComNig.