Ƙungiyar ma’aikatan wutar lantarki ta Najeriya ta ce za ta tsunduma yajin aiki sakamakon cire tallafin man fetur da gwamnatin Æ™asar ta yi.
Ƙungiyar ta ce ta ɗauki matakin ne bayan da ƙungiyar kwadogo ta ƙasar NLC ta sanar da matakin tsunduma yajin aiki sakamon cire tallafin man fetur da gwamnatin ƙasar ta yi, lamarin da ta ce ya haifar da ƙaruwar hauhawar farashin kayayyaki a ƙasar.
Shugaban ƙungiyar mai lura da shiyyar birnin tarayya Abuja da Kogi, Godfrey Aba ya tabbatarwa da BBC cewa ƙungiyar za ta shiga yajin aikin daga ranar Laraba 7 ga watan Yuni, matuƙar gwamnatin ƙasar ba ta janye matakin cire tallafin man ba.
Ya Æ™ara da cewa ”Æ™ungiyar za ta shiga yajin aikin ne har sai gwamnati ta janye matakin da ta É—auka”.
A cikin wata sanarwa da ƙungiyar ta fitar mai ɗauke da sannun muƙaddashin sakataren ƙungiyar na ƙasar Dominic Igwebike, ta yi kira ga mambobinta da su yi biyayya ga matakin ƙungiyar na tsunduma yajin aiki a tsakiyar makon da ke tafe.
Ƙungiyar ƙwadado ta ƙasar NLC dai ta ce za ta fara yajin aiki tare da zanga-zanga daga ranar Laraba mai zuwa a wani mataki na nuna rashin amincewarta kan cire tallafin man fetur da gwamnatin ƙasar ta yi.
Sabon Shugaban ƙasar Bola Ahmed Tinubu ne ya sanar da matakin cire tallafin man fetur ɗin a cikin jawabin da ya gabatar cikin makon jiya a lokacin bikin rantar da shi.
Ita ma dai kungiyar ‘yan jarida ta Æ™asar NUJ ta sanar da É—aukar makamancin wannan mataki a cikin wata sanarwa da ta fitar ranar Asaba.
BBC