Ɗalibai da yawa sun firgita da ƙarin kuɗin makaranta ninki biyu tashi guda, har ma ana fargabar wasu na iya watsar da karatunsu na jami'a.
Hukumomin jami'ar Bayero dai sun ce sun yi ƙarin ne saboda gwamnatin tarayya ta cire tallafin da take bai wa jami'o'i a ƙasar.
A cewar Mallam Lamara Garba, jami'in hulɗa da jama'a na Jami'ar Bayero, sanin kowa ne gwamnati wadda ita ce ke tafiyar da harkokin jami'o'i ta ce ta cire hannunta a fannin ilmi mai zurfi kamar yadda ta cire a fannin man fetur.
Ya ce bisa la'akari da wannan yanayi, babu yadda za a yi jami'o'i su iya tafiyar da al'amuransu, ba tare da sun ƙara kuɗi ba.
Wata ɗaliba da ke karanta fannin kimiyyar kwamfiyuta a jami'ar ta shaida wa BBC cewa a bara kuɗin da suka biya don yin rijista a matsayin sabbin ɗalibai, bai fi N35,000 ba, amma a jadawalin da aka fitar bana, sabon ɗabili sai ya biya N110,000.
Lamara Garba ya yi iƙirarin cewa Bayero ce take karɓar kuɗin makaranta mafi ƙaranci a tsakanin duk jami'o'in Najeriya.
"Akwai jami'ar da na sani, 350,000 ta caza a waccan shekarar karatu, amma mu kuma a nan gaba ɗaya ƙarin da muka yi N95,000 ne zuwa N170,000 mafi yawa."
Ya ce: "Idan ka yi la'akari.... Yanzu za ka ga misali a nan private secondary school, za ka ga yaro ana biyan N100,000 ko N200,000 ko N500,000 a term (wato a zango ɗaya) ba a shekara ba. Mu kuma wannan ƙari a shekara ne".