Majalisar Tarayya ta goma da aka buɗe baya-bayan nan a Najeriya, ta zo da sabbin al'amura a tarihin ƙasar.
Yayin zaɓen 2023, matasa sabbin jini sun kayar da wasu tsoffin 'yan majalisa da suka shafe tsawon lokaci suna wakilcin al'ummominsu.
Cikin abubuwan tarihin da aka gani a majalisa ta goma akwai samun matashin da ya fi ƙarancin shekaru da ya taɓa zama ɗan majalisar tarayya a tarihin Najeriya.
Ibrahim Mohammed mai wakiltar mazaɓar tarayya ta Birnin Kebbi/ Kalgo/ Bunza a jihar Kebbi ya yi nasarar cin zaɓe ne yana da shekara 26 a duniya.
To, ko me ya yi masa ƙaimi ya shiga harkokin siyasa?