Mazauna jihar Enugu sun bijirewa umarnin gwamnatin jihar na yin watsi da umarnin zama a gida na ranar Litinin da haramtacciyar ƙungiyar IPOB ta bayar.
Gidan Talabijin na Channels TV ya bayar da rahoton cewa, tituna, makarantu, bankuna, kasuwanni, da sauran wuraren taruwar jama'a sun kasance ba kowa a yau Litinin.
Gwamnan jihar, Peter Mbah, a ranar 1 ga watan Yuni ya ayyana "ba za a sake yin zaman gida ba a Enugu," daga ranar Litinin, 5 ga watan Yuni.
"Wannan shine a sanar da dukkan makarantu, kasuwanni, kantuna, asibitoci, masu sufuri, manyan kantuna da sauran jama’a cewa, duba da yadda gwamnatin jihar Enugu ta hana/ soke dokar zaman-gida a kwanakin baya a kowane lungu da sako na jihar, an umurce su da su rika gudanar da harkokinsu na yau da kullum a kowane mako, ciki har da ranar Litinin,” in ji sanarwar.
Mista Mbah ya bayyana cewa, gwamnatinsa za ta shirya tsaf domin tattaunawa da mutanen da ke da koke-koke na gaskiya domin samar da dawwamammen zaman lafiya da tsaro a jihar Enugu, inda ya kara da cewa wannan odar na rage nagarta da tattalin arziki ga jama’a.
Jaridar DAILY NIGERIAN ta ruwaito cewa mazauna jihar da dama sun rasa rayukansu saboda karya dokar zaman gida da kungiyar ta haramta.