Liman Mohammad, jami’in kula da jigilar aikin hajji na 2023 Aero Contractors ne ya bayar da tabbacin a cikin wata sanarwa.
Mohammed ya ce hukumar alhazai ta kasa NAHCON ta ware maniyyata 8,033 ga kamfanin domin jigilar su zuwa kasar Saudiyya.
A cewarsa, mahajjatan sun fito ne daga jihohin Nasarawa da Oyo da Adamawa da kuma Taraba.
Ya ce tuni kamfanin ya kammala jigilar dukkan alhazan jihar Nasarawa zuwa Saudiyya.
Jami’in ya kara da cewa ya zuwa yanzu, kamfanin ya yi jigilar maniyyata 2,748 daga jihohin Nasarawa da Oyo.
Ya ce kamfanin ya koma Legas inda zai yi jigilar maniyyata kusan 1,500 daga jihohin Oyo da Legas a cikin sawu biyar.
Mista Mohammed ya ce, kamfanin jirgin ya kuduri aniyar kammala jigilar dukkan alhazan da aka ware masa zuwa ranar 12 ga watan Yuni, mako biyu kafin rufe filin jirgin sama na Jeddah.
“Don haka daga ranar 12 ga watan Yuni za mu samu ‘yanci. Za a rufe filin jirgin sama na Jeddah a ranar 26 ga watan Yuni, wato kimanin kwanaki 14 da kammala aikinmu, da yardar Allah,” inji shi.