A wata sanarwa da jami'in hulda da jama'a na hukumar Femi Babafemi ya fitar ya ce hukumar ta samu bayanan sirri game da wata babbar mota É—auke da tabar.
Ya ce nan take jami'an hukumar suka yi wa motar kwanton É“auna tare da kama buhu 50 na tabar wiwi da nauyinta ya kai kilogiram 2,434.1 a kan babbar hanyar Epe zuwa Lekki da ke jihar.“Direban motar ya fice daga cikinta, inda ya shiga wata karamar mota Æ™irar Hilux da ke yi wa babbar motar tasa rakiya'', in ji sanarwar.
Haka kuma sanarwar ta ci gaba da cewa a ranar Talatar da ta gabata jami'an hukumar sun kama wani jirgin ruwa ɗauke da tabar da nauyinta ya kai kilogiram 2,910 a wurin shaƙatawar gaɓar tekun Alfa a lokacin da ya isa ƙasar daga Ghana.