Oluremi Tinubu, uwargidan shugaban kasa Bola Tinibu, a yau Litinin a Abuja, ta shiga ofishin ta a matsayin uwargidan shugaban kasar Najeriya.
Misis Tinubu da ta isa bangaren uwargidan shugaban kasa ta samu rakiyar mataimakanta na tsaro.
Uwargidan shugaban kasa a lokacin da ta isa wurin, ta samu tarba ne daga babban sakatare na fadar shugaban kasa, Mista Tijjani Umar da sauran shugaban rukunai a ofishin uwargidan shugaban kasa.
Daga nan Tinubu ta jagoranci rangadin wasu ofisoshi da ke cikin bangaren uwargidan shugaban kasa, wanda ya hada da sassan gudanarwa, bangaren fasahar zani, sashen girke-girke, yaɗa labarai da sashin shirya tafiye-tafiye.