Yan Sanda Sun Kwace Motocin Gwamnati A Gidan Tsohon Gwamnan Zamfara
Wata majiya tace tsohon gwamna Matawalle a ranar Juma'a jami'an tsaro suka dira a gidan matawalle inda suka kwato motoci na alfarma mallakin gwamnatin jihar.
’Yan sanda sun kai samame gidan tsohon gwamnan Zamfara, Muhammad Bello Matawalle, inda suka kwace motocin alfama na gwamnati da ake zargin ya yi awon gaba da su bayan ya sauka daga mulki.
Majiyar tace ba ta tantance iya adadin motocin da aka kwace daga gidan Matawalle ba, amma majiyarmu ta tabbatar mana cewa jami’an tsaro sun yi awon gaba da motocin alfarma guda hudu daga gidan.
Shi ma jami’in yada labaran Matawalle, wato Zailani Bappa, mun kasa samun sa, har zuwa lokacin da aka kammala wannan rahoto.
majiyar ta ruwaito yadda kwana biyu bayan rantsar da sabon gwamnan jihar, Dauda Lawal, ya zargi Matawalle, da yin awon gaba da motocin alfarma guda 17 na ofishin gwamna da na mataimakin gwamna da cewa mallakinsa ne.
Gwamna Lawal ya ce, hatta kayan ofis da talabijin da kuma murahun girkin gidan gwamnati, Matawalle bai bari ba.
A ranar Asabar ya ba wa tsohon gwamnan wa’adin kwana biyar ya dawo da duk kadarorin gwamnatin da ya yi awon gaba da su.