Rundunar Yansandan Kano ta sake kama mutane 57 da take zargi da balle shagunan Alumma domin wawure musu dukiyoyinsu.
Kakakin rundunar yansandan Kano, SP Abdullahi Haruna Kiyawa ne ya sanar da hakan ta cikin wata sanarwa daya aikowa Nasara Radio.
Idan baku Manta ba, a kwanan nan rundunar ta kama 47, inda ta gurfanar dasu a gaban kotu kan wawure dukiyoyin Alumma.