A ranar 8 ga watan Juni 1998 janar Sani Abacha ya rasu.
Rasuwarsa a wancan lokacin ta girgiza jama'a musamman ganin cewa bai kwanta jinya ba.
Marigayin ya rasu ne a jajibirin ranar da ya gudanar da ayyukansa kamar yada ya saba a matsayinsa na kwamandan askarawan Najeriya.Uwargidansa Maryam Abacha ta ce iyalinsa na yi wa marigayin adu'o'i a duk ranar zagayowar mutuwarsa.
"Muna adu'o'i da mu da mutanen gida da limamanmu na gida, mu na fida’u, mu na mi shi adu'o'i" a cewarta.
Hajiya Maryam Abacha ta kuma ce rayuwarsa da iyalinsa ta sha banban da aikinsa na soja.
A cewarta marigayin mutum ne mai son yin raha da iyalinsa da kuma motsa jiki.
"Zai tashi da safe ya yi adu'a irinta adininsa, ya shirya ya tafi wurin aiki kuma ya dawo ya ci gaba da harkokinsa", in ji ta.
BBC