Matakin na zuwa ne bayan sabon shugaban ya sanar da matakin sallamar hafsoshin da ke jagorantar rundunonin tsaron ƙasar daga aiki nan take.
Wata sanarwa da Mista Willie Bassey, daraktan yaɗa labarai a ofishin Sakataren Gwamnatin Tarayya ya fitar, ta bayyana Mallam Nuhu Ribaɗu a matsayin Mashawarcin shugaban ƙasa kan harkar tsaro wato National Security Adviser.
An yi ta muhawara kwanan baya, lokacin da Tinubu ya sanar da sunan tsohon shugaban hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa EFCC a matsayin mai bai wa shugaban ƙasa shawara na musamman kan harkar tsaro.
Da wannan sanarwa, Mallam Nuhu Ribaɗu dai zai gaji Manjo Janar Babagana Mongunu (mai ritaya).
Shugaban Najeriyar dai ya naɗa Manjo Janar C.G Musa a matsayin babban hafsan tsaro, bayan sallamar Laftanal Janar Lucky Irabor.
Sai kuma Manjo Janar T. A Lagbaja a matsayin babban hafsan sojin ƙasa na Najeriya, inda ya canji Laftanal Janar Faruk Yahaya.
Haka zalika, Rear Admiral E. A Ogalla ya zama babban hafsan sojin ruwa na Najeriya, inda ya maye gurbin Vice Admiral Awwal Zubairu Gambo.
Akwai kuma Air Vice Marshal H.B Abubakar a matsayin sabon babban hafsan rundunar sojojin sama na ƙasar, inda ya gaji Air Marshal Oladayo Amao.
Ƙarin manyan jami'an tsaron har da DIG Kayode Egbetokun a matsayin Babban Sufeton 'Yan sandan Najeriya, inda ya maye gurbin Usman Alƙali Baba.
Haka kuma sanarwar ta ce Shugaba Tinubu ya naɗa Manjo Janar EPA Undiandeye a muƙamin babban hafsan tattara bayanan sirri na tsaro wato Defence Iintelligence.