A ranar Alhamis, 22 ga watan Yuni, 2023, Bola Tinubu zai yi ziyararsa ta farko zuwa kasashen waje tun bayan rantsar da shi a matsayin sabon shugaban Najeriya a ranar 29 ga Mayu, 2023.
Shugaban zai hadu da shugabannin kasashen duniya a birnin Paris na kasar Faransa, in ji mai ba shi shawara na musamman kan ayyuka na musamman, sadarwa da dabaru, Dele Alake.
A cikin wata sanarwa a ranar Litinin, Alake ya ce shugaban zai bi sahun sauran shugabannin duniya don yin nazari tare da rattaba hannu kan wata sabuwar yarjejeniya ta hada-hadar kudi ta duniya wacce ta sanya kasashe masu rauni a jerin fifiko don tallafawa da saka hannun jari, sakamakon mummunan tasirin sauyin yanayi, matsalar makamashi, da kuma bayan tasirin cutar COVID-19. Taron wanda shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron zai karbi bakunci, zai gudana ne a Palais Brongniart.
A cewar mashawarcin shugaban kasar, taron na kwanaki biyu zai duba damar da za a maido da harkokin kudi ga kasashen da ke fuskantar kalubalen kudi na gajeren lokaci, musamman wadanda suka fi fama da basussuka; shirya samar da sabbin kudade ga kasashen da ke fama da sauyin yanayi; samar da ci gaba a cikin kasashe masu karamin karfi, da karfafa zuba jari kan ababen more rayuwa na "kore" don sauyin makamashi a kasashe masu tasowa da masu tasowa, shugaban zai kasance tare da mambobin kwamitin ba da shawara kan manufofin shugaban kasa da manyan jami'an gwamnati. Zai dawo Abuja ranar Asabar.” Inji Alake. A yayin haka kuma, a ranar Litinin shugaban ya gana da hamshakin attajirin Afrika Aliko Dangote da kuma shugaban gidauniyar Bill & Melinda Gates, Bill Gates a fadar gwamnati da ke Abuja.
Ziyarar dai wani bangare ne na kudirin gidauniyar Gates na yin hadin gwiwa da al’umma da shugabanni domin tallafa wa kirkire-kirkire da kuma tattauna harkokin kiwon lafiya da ci gaban duniya tare da shugabannin kasa da na kananan hukumomi.