Majalisar dokokin jihar ta tabbatar da sunayen kwamishinonin da ta tantance a jiya Laraba, biyo bayan wata wasika da gwamnan jihar Engr. Abba Kabir Yusuf, yana neman amincewar majalisar don tantancewa tare da tabbatar da wadanda aka zaba domin nada a matsayin mambobin majalisar zartarwa.
Majalisar a zamanta na yau wanda shugaban majalisar Rt. Hon. Isma’il Jibrin Falgore ya tabbatar da nadin wadanda aka nada a cikin kudirin da shugaban masu rinjaye Hon. Lawan Husaini Dala wanda aka tattauna a kwamitin gaba daya majalisar ta tattauna kuma ta amince da tabbatar da hakan.
Majalisar ta tabbatar da sunayen mutane goma sha bakwai inda sauran biyun za a tabbatar da su idan sun dawo gida daga aikin Hajji.
Ƙarin bayani.......
A zaman majalisar na yau Alhamis,shugaban majalisar Rt.Hon.Ismail Jibril Falgore ya karanto sunayen Yan kwamitin da zasu nada sauran kwamitin.
1.Rt.Hon Ismail Jibril Falgore,(Shugaban)
2.Muhammad Bello Butu -butu(mataimakin shugaban)
3.Ali Maje Akawun majalisa(sakatare)
Bayan amincewa da gida yayi na kafa wannan kwamati ne sai shugaban majalisar Hon Falgore ya umurci shugaban masu rinjaye na majalisar daya karanto sunayen Kwamishinonin goma sha shida da majalisar ta tantance kamar haka-
1Hon.Umar Haruna Doguwa
2.Hon. Ali Haruna makoda
3.Dr.Abubakar Labaran Yusuf
4.Dr.Danjuma Mahmud
5.Hon.Musa Suleman Shanono
6.Hon.Abbas Sani Abbas
7.Ladidi Ibrahim Garko
8.Engr. Marwan Ahmad
9.Hon.Muhammad Diggol
10.Hon Adamu Ali Kibiya
11.Dr.Yusuf Ibrahim k/Mata
12.Hon.Safiyanu Hamza
13.Tajuddeen Othman Ungogo
14.Hon Nasiru Sule Gari
15.Barr.Haruna Isa Dederi
16.Baba Halilu Dantiye.
Bayan karanto su daya bayan daya ne Yan majalisar suka amince dasu nan take a matsayin wadanda mai girma Gwamna zai rantsar a matsayin kwamishinoni.
Daga karshe an dage zaman majalisar zuwa 17 ga watan Yuli Mai kamawa.
Bayan zaman majalisar ne Hon Lawan Usaini Cediyar Yan gurasa wato Shugaban masu rinjaye na majalisar ya mana Karin bayani dangane da amincewa da majalisar tayi na kwamishinonin.