Tirƙashi: Muhuyi Magaji Rimin Gado yana daga cikin wanda aka baiwa Fili kyauta a Gwamnatin Ganduje, Cewar mutanen tsohuwar gwamnatin jihar kano ƙarƙashin jagorancin Dr. Abdullahi Umar Ganduje.
Wannan sheda ta takardu dai ta fito bayan da shugaban Hukumar karbar ƙorafe-ƙorafe ɗa daƙile cin hanci da rashawa ya koma kan kujerar sa domin ƙarashe sauran shekaru biyun sa kamar yadda kotu ta bada unarni tun zamanin mulkij Dr. Abdullahi Umar Ganduje inda jim kadan bayan komawar tasa ne yayi iƙirarin cigaba da bincikar Matar tsohon Gwamnan Jihar kano Proff. Hafsat Umar Ganduje tare da iƙirarin cigaba da binciken faifan bidiyon dala na tsohon Gwamnan.
A cewar wata majiya ta sirri mai ƙarfi Gwamnan tace Gwamnan Kano Engr. Abba Kabir Yusuf ya bada umarnin bin diddigin wasu al'amura na shugaban hukumar wanda suke a gaban kotu domin tabbatar da kuma samar da gaskiya kan ƙararrakin da aka shigar gaban kotu a kan Muhuyin domin tantance gaskiyar sa kasancewar gwamnati ce mai adalci kamar yadda take iƙirari.