Kabiru Basiru Fulatan
Wani al’amari mai kama da almara ya faru a Kano, inda aka zargi wani waliyin amarya da sace sadaki.
An sace kudin sadakin ana tsaka da daurin aure a unguwar Kurna dake birnin Kano.
Majiyar Gaskiya Ta Fi Kwabo ta bayyana cewa, an dakatar da daurin auren yayin da kowa yayi cirko-cirko, bayan da aka nemi sadakin amarya aka rasa.
Rahotanni sun bayyana cewa, jim kadan da faruwar wannan lamari ne sai aka fara ‘yar caje, inda nan da nan aka samu kudin a aljihun babbar rigar waliyin amaryar.
Sai dai ya ce, shi fa bai san yadda aka yi kudin suka shiga aljihunsa ba.
Daga karshe dai an tasa waliyin amarya zuwa waje, sannan aka kira kaninsa ya maye gurbinsa, aka daura auren.