Tsohon gwamnan jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ya nemi babbar Kotun tarayya dake zaman ta a Kano, kan cewa ta dakatar da hukumar yaƙi da masu yiwa tattalin arzikin ƙasa zagon ƙasa ta EFCC daga bincikarsa kan bidiyon da ya nuna shi yana karbar dollars (kuɗaɗen ƙasar Amurka) a hannun dan kwangila, kuma ake zargin na rashawa ne.