A cikin sanarwar Shugaban Kungiyar ta CAN Daniel Okoh ya mika ta'aziyyarsa ga iyalan mamacin.
Kungiyar ta yi kira ga gwamnati da ta tabbatar da kare kowane irin dan kasa ba tare da la'akari da addinin da yake ba.
Rabaran John Joseph Hayep shi ne shugaban kungiyar reshen jihar Kaduna, kuma ya shaida wa BBC cewa babban dalilinsu na fitar da wannan sanarwa shi ne jan hankalin jama'a da su rika daukar matakin mika duk wanda ake zargi da laifi ga hukuma, maimakon daukar matakihaka nan ba tare da bincike ba.
''A baya mun lura idan aka kashe Musulmi sai Kirista ya yi shiru, idan aka kashe Kirista sai Musulmi ya yi shiru, don haka muke ganin cewa mu ƴan Najeriya ne, dole ne Kirista ya kare Musulmi, shi ma Musulmi ya kare Kirista'' in ji shi.
Wannan abu da ya faru ba dai-dai ba ne, domin ya saba da koyarwar addini, kuma muna mika ta'aziyya ga iyalinsa, Allah ne kaɗai Ya san halin da suke ciki yanzu, ba za ka iya kwatanta yadda suke ji ba'' a cewar shugaban.
Ya kara da cewa dole ne a kara ilmantar da jama'a cewa idan ana zargin mutum, hakan ba wai yana nufin ya aikata laifin ba ne har sai an yi bincike an tabbatar da abin da ake zargin shi da aikatawa.
Ƙungiyar Kiristocin ta kuma bukaci jami'an tsaro su kama waɗanda suka kashe mutumin, domin hakan ya zama izina, sannan kuma a kare aukuwar irin hakan a gaba.
Yadda lamarin ya faru:
Shi dai marigayi Usman Buda wanda mahauci ne a cikin garin Sokoto, ya rasa ransa ne sakamakon musayar ra'ayi da fahimta da ta shafi addini, inda wasu da ba su fahimce shi ba suka ce ya yi ridda daga karshe suka far masa da duka har suka halaka shi da jifa da duwatsu, kamar yadda aka gani a bidiyon da ya yadu a shafukan sada zumunta.
Ƴan sanda sun ce sun samu kiran gaggawa yayin da lamarin ya faru, inda suka kai dauki, sai dai waɗanda suka aikata kisan a lokacin sun gudu, kana suka dauki Usman Buda zuwa asibitin koyarwa na Jami'ar Usman Danfodiyo da ke Sokoto, a can aka tabbatar masu da cewa ya rasu.
Jami'in hulda da jama'a na rundunar yan sandan jihar ya ce an fara bincike don daukar mataki a kan lamarin.