......Ba za a rantsar da wani Kwamishina ba ba tare da bin ka'idar aiki ba - Abba Gida Gida
Gwamnan Jihar Alhaji Abba Kabir Yusuf ya umurci dukkan wadanda aka nada na kwamishinoni 19 su bi ka’idojin da’a.
Ta wannan sanarwar, ana sa ran wadanda aka zaba za su bayyana kadarorinsu a cikin mafi kyawun lokaci kafin a fara tantance su a majalisar dokokin jihar a ranar Alhamis 22 ga watan Yuni, 2023 da karfe 10 na safe a harabar majalisar dokokin jihar.
Gwamnan ya sha alwashin cewa babu wani kwamishina da za a rantsar da shi a matsayin mamban majalisar ministoci ba tare da cike fom din bayyana kadarorinsa daga ofishin Code of Conduct Bureau ba.
"Duk sauran masu rike da mukaman siyasa a karkashin wannan gwamnati su ma za su bi umarnin da aka ba su."
Gwamna Abba Kabir Yusuf na fatan jaddada aniyarsa ga mutanen jihar Kano nagari cewa gaskiya da rikon amana ya kasance tushen tsarin gwamnatinsa wanda za a yi amfani da shi wajen ganin an samar da kyakkyawan shugabanci kamar yadda ya yi alkawari a tsarinsa a lokacin yakin neman zabe.
Sa hannu
Sanusi Bature Dawakin-Tofa
Babban Sakataren Yada Labarai na Gwamnan Jihar Kano.