Wani abin jeje ya faru a ranar Litinin yayin da wasu ‘yan jam’iyyar All Progressives Congress guda biyu daga jihar Imo suka yi tattaki zuwa Abuja domin bikiin kaddamar da majalisar wakilai ta kasa karo na 10 a ranar Talatar nan a wani hatsarin mota da ya rutsa dasu a hanyar Agbor a jihar Delta.
Motar da ke dauke da su, kamar yadda jaridar DAILY POST ta bayaana rahoton afkuwar al'amarin inda mitar tasu ta daki wata motar dake tafe a Agbor, jihar Delta.
An tabbatar da mutuwar mutane biyu a cikin motar ambulance. A cewar majiyoyin jam’iyyar, yayin da wasu da suka samu raunuka daban-daban aka kai su asibiti.
Wakilinmu ya tattaro cewa wasu mutane biyu daga karamar hukumar Isiala Mbano da ke yankin Amaraku na jihar sun mutu a hadarin mota.
Wadanda abin ya shafa a cewar wani jami’in jam’iyyar da ya nemi a sakaya sunansa, su ne kodinetocin Patrick Ndubueze, zababben Sanata mai wakiltar Imo ta Arewa da Mirriam Onuoha, zababben wakiliyar mazabar tarayya ta Okigwe ta Arewa.
Kakakin jam’iyyar APC na jihar, Cajetan Duke, ya tabbatar da faruwar lamarin yayin da aka tuntube shi.
Ya kara da cewa mutane biyu ne kawai jam’iyyar ta tabbatar da mutuwarsu.