Ƙudurin zai kuma shafi gwamnoni da mataimakansu da 'yan majalisa da alƙalai da sauran masu riƙe da muƙaman gwamnati.
Ta ce ƙarin wanda aka yi a kan tsagwaron albashi (ban da alawus-alawus) ya kai kashi 114, abin da ke nufin shugaban ƙasa zai iya karɓar albashin da ya kusan kai naira miliyan biyu duk wata.
Shugaban hukumar (RMAFC) Muhammadu Shehu ya faɗa wa BBC cewa sun yi nazari bisa la'akari da halin da ake ciki a ƙasa, kafin yin ƙarin albashin.
Sai dai a cewarsa, matakin ƙuduri ne kawai don kuwa sai an gabatar wa Majalisar Tarayya don amincewa kafin ya zama doka.
Haka zalika ƙarin zai shafi ministoci da kwamishinoni da mataimaka na musamman kamar yadda sashe na 84 da sashe na 124 na tsarin mulkin Najeriya ya tanada.
A cewar hukumar, karon ƙarshe da aka yi wa zaɓaɓɓun 'yan siyasar ƙarin albashi a Najeriya, shi ne shekara ta 2007.