Tun a shekarar 2020 Majalisar Dattawa ta amince da ƙudirin mai taken The Prevention, Prohibition and Redressal of Sexual Harassment in Tertiary Educational Institutions Bill amma ƙunshe da tanade-tanade daban.
Shugaban kwamatin Majalisar Dattawa kan harkokin shari'a, Sanata Opeyemi Bamidele, ya ce taron gamayyar 'yan majalisar ya haɗe kan tanade-tanaden biyu kafin ya gabatar da rahotonsa a zauren Majalisar ranar Laraba.
Cikin tanadin dokar, akwai matakan daƙile yunƙurin aikata lalata da kuma cin zarafi na jinsi a dukkan matakin karatu na gaba da firamare a Najeriya.
Mataki na gaba shi ne miƙa kundin dokar ga Shugaba Bola Tinubu don ya saka mata hannu kafin ta zama doka a ƙasar.