Adesola ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da Daraktan Yada Labarai da Sadarwa na FCT, Muhammad Sule, ya fitar a Abuja a yau Lahadi.
A cewar sanarwar, Mista Adesola ya yi magana ne a wajen bude bikin ranar keke ta duniya ta 2023 a Abuja.
Ya ce dama can an riga an fitar da hanyoyin keke a tsarin fitar da Abuja, inda ya kara da cewa yanzu sai dai a yi aikin gina hanyoyin.
“Wannan matakin zai zurfafa kamfen don rage tasirin sauyin yanayi, za a rage fitar da hayaki a ababe hawa idan aka karfafa hawa keke,” in ji shi.