Sanatocin jam'iyun adawa sun sha
alwashin kin amincewa da duk wani yunkuri na kawo cikas ga shugabancin marasa rinjaye a majalisar dattawa.Manyan mukamai hudu da aka ware wa jam'iyyun adawa a Majalisar Dattawa su ne shugaban marasa rinjaye da mataimakinsa da mai tsawatarwa da kuma mataimakinsa.
A cikin wata sanarwar haɗin gwiwa da sanatocin suka fitar, sun ce ɓangaren marasa rinjaye na majalisar dattawan za su zaɓi shugabanninsu bayan tuntubar jam'uyyunsu ba tare da katsaladan daga wurin wasu da ke adawa da tsarin mulkin dimokuradiyya ba.
Sun nanata cewa har yanzu babu wani sanata da aka amince da shi ko aka zaɓa a matsayin wanda za a bai wa waɗanan mukamai.