Tun farko an tsara Tinubu zai koma gida Abuja ne bayan kammala taron, wanda shugabannin Afirka suka tattauna harkokin kasuwanci da zuba jari a nahiyar.
"Sai dai yanzu zai wuce birnin Landan na Birtaniya don yin wata ziyara ta ƙashin-kansa," a cewar sanarwar.
Ta ƙara da cewa shugaban zai koma gida kafin bikin Idin Babbar Sallah, wanda za a fara ranar Laraba.
A ranar Talata Tinubu ya tafi Paris bisa rakiyar wasu daga cikin masu ba shi shawara.