Gwamna Abba Kabir Yusuf ne ya bayyana hakan yayin da yake karɓar baƙuncin Sarkin Gaya Aliyu Ibrahim lokacin da ya kai wa gwamnan gaisuwar Sallah a yau Lahadi.
"Na yi amfani da damar na faɗa wa sarkin da al'umma cewa za mu sake buɗe Asibitin Yara na Hasiya Bayero nan da mako biyu masu zuwa don amfanin jama'a," in ji shi ckin wani saƙon Twitter.
An rufe asibitin ne bayan tsohuwar gamnatin Abdullahi Umar Ganduje ta haɗe shi da asibitin Isiyaka Rabiu da ke kan titin Gidan Zoo, wanda shi ma na yara ne, amma a tsarin haɗin gwiwa tsakanin gwamnati da 'yan kasuwa.
Sai dai sabuwar gwamnatin NNPP ƙarƙashin Abba na zargin tsohuwar gwamnatin da sayar wa wani ɗan kasuwa da asibitin. Hakan ta sa aka karɓe kuma aka gyara tsohon ginin da zimmar ci gaba da ayyuka a ciki.