Alhazan Najeriya da suka mutu a aikin hajjin bana sun kai 13, kuma wasu 41,632 suka kamu da rashin lafiya a kasar Saudiyya.
Shugaban jami'an likitocin Najeriya mai kula da alhazan ƙasar, Dr Usman Galadima ne ya bayyana hakan a daren Lahadi a birnin Makkah yayin taron bibiyar yadda al'amura ke tafiya bayan Arafat.
A jawabinsa, Dr Galadima ya bayyana cewa, jimillar mahajjata bakwai ne suka rasu kafin Misha’ir – tafiya daga Mina zuwa Arafat, da komawa Mina – yayin da wasu shida kuma suka rasu a lokacin Misha’ir.
Ya ba da shawarar a riƙa yi wa maniyyata cikakken gwajin lafiya kafin tafiya aikin Hajji tare da ba da takardar shaidar cewa suna cikin ƙoshin lafiya.
Ya ce kamata ya yi a hana tsofaffin alhazai da majinyata marasa lafiya daga zuwa Jamarat (wurin da alhazai ke jifan shaidan).
Ya kuma buƙaci a riƙa aiwatar da hada-hadar mahajjata kamar yadda hukumomin Saudiyya suka ba da shawara.
Ya buƙaci jihohin da ke da motocin ɗaukar marasa lafiya su gabatar da su don aiki tare da jami'an likitocin kula da mahajjata na ƙasa don samun ƙarin haɗin kai a kan lamuran da ke buƙatar gaggawa.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa kwamishinan hukumar alhazai ta ƙasa mai kula da harkokin sufurin jiragen sama, Goni Sanda na cewa za a fara jigilar maniyyatan Najeriya zuwa gida, daga ranar Talata 4 ga watan Yuli sannan kuma a kammala ranar 3 ga watan Agusta.