"Saboda babu abin da ya fi nasara, a yau ina sanar da ku cewa zan tsaya takara,” in ji Bongo lokacin da yake jawabi ga magoya bayansa.
A ranar 26 ga watan Agusta za a yi zaben shugaban ƙasa a Gabon.
Bongo mai shekaru 64, ya kasance shugaban Æ™asar ta Gabon mai arzikin man fetur tsawon wa’adin mulki na shekaru bakwai har sau biyu.
Ya gaji mahaifinsa, Omar Bongo wanda ya rasu a shekara ta 2009, kuma mahaifin na sa ya jagoranci ƙasar tun daga shekarar 1967 har zuwa rasuwarsa.
Kundin tsarin mulkin Gabon bai iyakance wa’adin mulkin shugaban Æ™asa ba.
A zabuÆ™a biyu da Ali Bongo ya samu nasara, ya fuskanci Æ™alubale daga wajen ‘yan adawa inda suka yi zargin an tafka magudi.
A shekara ta 2016, lokacin da ya lashe zaben shugaban ƙasa, sai da aka yi zanga-zanga a ƙasar har aka ƙona ginin majalisar dokoki.
Sanarwar Ali Bongo ta neman tazarce ta jefa shakku a zukatan al‘ummar Æ™asar ganin cewa yayi fama da bugun jini a watan Oktoban 2018 har sai da aka kai shi Moroko neman magani.
Ya shafe watanni uku yana jinya a ƙasar waje, amma sai ya koma gida ba zato ba tsammani a lokacin da aka yi yunkurin kifar da gwamnatinsa.