Ɗaliban sun ce karatu na neman ya gagare su saboda kuɗin karatun ya ƙaru da fiye da kashi 60 cikin ɗari.
Daliban dai masumman ma masu ɗaukar ɗawainiyar kansu sun bayyana cewa suna jin jiki wajen biyan kuɗin karatu ba don jami`o`in Birtaniya sun kara musu kuɗi ba, sai don ddunkule tsarin canjin kuɗi da babban bankin Najeriyar ya yi.
Matakin dai ya yi sanadin jingine amfani da tsohon farashin gwamnati mai kama da tallafi na naira 471 a kan dala ɗaya, wanda yanzu aka bar kasuwa ta yi halinta.
Lamarin ya jefa ɗaliban cikin kunci da halin kaka-nika-yi kasancewar a halin da ake ciki dala ɗaya ta kai naira 750, yayin da fam ɗaya yake tashi a kan naira 957.
Wani dalibi da ya nemi a sakaya sunansa, ya ce sabon tsarin canjin kuɗin, ya sa sai sun yi da kyar da jiɓin goshi suke samun abin da za su yi ciko da shi wajen biyan kuɗin makaranta, hakan ta sa wasu ɗaliban suke rungumar hanyoyi daban-daban na yin kwadago domin su ƙara nauyin lalitarsu abin da kuma ke iya raba musu hankali a karatun da suka je yi.
A watan Yunin wannan shekara ne babban bankin Najeriya ya ɗauki matakin dunkule tsarin canjin kuɗi, inda gwamnati ta yi bankwana da tsarinta na kayyade farashin dala, inda yanzu aka bar kasuwa ta yi halinta.