Wata sanarwa da shugaban kwamitin amintattu na Amnesty International a Najeriya, Auwal Musa Rafsanjani ya fitar, ta ce Isa Sanusi zai jagoranci fadada ayyukan bincike da gangamin kungiyar a Najeriya.
Zai kuma mayar da hankali a kan al'amuran da suka shafi rikice-rikice da ilmi da kare hakkin dan'adam da daidaiton jinsi da sauyin yanayi da shigar da matasa cikin harkokin ingantawa da kare hakkin dan'adam.
“Nadin Isa Sanusi a matsayin daraktan kasa zai karfafa tasirin kungiyar Amnesty International a Najeriya.
Yana da gogewar aiki ta tsawon shekara bakwai, abin da ke nufin zai ba da gudummawa wajen ci gaba da ganin tasirin ayyukan Amnesty a Najeriya,” in ji Auwal Musa Rafsanjani.
Kafin sabon nadin nasa, Isa Sanusi shi ne manajan yaɗa labarai da sadarwa na Amnesty International a Najeriya, mukamin da yake rike da shi tun 2016. Ya kuma taɓa aikin jarida da BBC tsawon shekara 10, sannan ya taɓa zama mataimakin editan jaridar Daily Trust.
Mallam Isa ya kuma jagoranci ayyukan kare hakkin dan'adam iri daban-daban da horar da masu fafutukar kare hakkin dan'adam a Najeriya.
Ya yi digirin farko a fannin Ingilishi a Jami’ar Bayero Kano sannan yana da digiri na biyu a fannin aikin jarida daga Jami’ar Landan.