Cikin wata sanarwa da kamfanin ya fitar a ranar Litinin, ya ce jirgin mallakin wani kamfanin Najeriya mai suna MT-TURA II, ya kai shekaru 12 ya na dakon irin wannan man a boye, kuma a yanzu za a lalata jirgin don ya zame wa masu irin wannan sana'a darasi.
Bangaren man fetur na Najeriya na fama da rashawa tsawon gwammam shekaru, inda ake satar danyen mai da kuma kafa haramtattun matatun mai a yankin Neja-Delta. A 2022 gwamnatin kasar ta ce tana asarar sama da gangar danyen mai 470,000 a kowace rana sanadiyyar wadannan ayyuka.
A watan Agustan 2022 danyen man fetur da Najeriya ke fitarwa ya ragu zuwa kasa da ganga miliyan guda a kowace rana - mafi karanci a cikin shekaru 30.