Ƴan sanda a jihar Ondo sun kama wata mata mai suna Esther Godwin bisa zargin watsa wa budruwar mijinta mai suna Endurance Samuel ruwan zafi ruwan zafi, bayan da ta zarge ta da cin amanar aure.
Lamarin ya faru ne a karamar hukumar Idanre na jihar ta Ondo.
Da yake magana kan lamarin, Endurance ta musanta yin mu'amala da mijin matar, inda ta ce tayi aiki ne da mijin matar a gonarsa domin taimaka masa.
“Esther ta kirani daga wajen da nake koyon aikin ɗi
nki inda ta faɗa min cewa na zo na karɓi manja da nake bin mijinta. Ina taya mijinta da wasu manoma aiki a gonakinsu.
“Na yi sauri na fita daga cikin shagon maigidana cikin farin ciki, ba tare da sanin cewa a ce za ta yaudareni zuwa shagon da take sayar da abinci domin zuba min ruwan zafi kan laifin da ban aikata ba," in ji Endurance.
Mijin matar da aka kama, Godwin, ya musanta batun cewa yana cin amanar matarsa.
“Ni nake biyan kuɗin asibitin budurwar da aka watsa wa ruwan zafi tun da lamarin ya faru," in ji shi.
Mai magana da yawun ƴan sandan jihar, Funmilayo Odunlami, ta ce tuni suka tura matar zuwa kotu domin fara sauraron shari'ar.