Zanga-zangar da aka yi a makon da ya gabata, ta janyo mutuwar akalla mutum 14.
Ministan harkokin cikin gidan ƙasar ya ce gwamnati ta samu bayanan sirri da ke nuna cewa wasu ɓata-gari na shirin kai wa jama'a hare-hare a ranar Laraba da kuma kan jami'an tsaro da ke kusa da wasu makarantu a Nairobi da kuma lardin Mombasa.
Shugaban ƴan sandan ƙasar ta Kenya Japheth Koome ya ayyana zanga-zangar ta adawa da ƙarin kuɗin haraji a matsayin haramtacciya, duk da cewa a wata babbar kotun a ƙasar ta yi watsi da yunkurin ayyana zanga-zangar haramtacciya a ranar Litinin.
Ƴan sanda sun harbe mutum goma yayin irin wannan makamanciyar zanga-zangar a ranar Laraba da ta gabata, .
An kuma fesa wa yaran makaranta sama da 50 hayaki mai sa hawaye lokacin da suke ɗaukar darussa a Nairob, inda daga bisani aka garzaya da su zuwa asibiti.
Akwai rahotanni da ke nuna cewa ƴan sanda na fesa hayaki mai sa hawaye kan masu zanga-zanga a Nairobi.
Masu zanga-zanga riƙe da maƙamai sun toshe hanyoyi a kudancin ƙasar inda suke karɓar kuɗi a hannun musu wucewa.
Kungiyoyin kare hakkin ɗan adam sun soki ƴan sanda kan abin da suka kira amfani da karfi fiye da ƙima.
Kungiyoyin cikin gida da na ƙasashen waje da kuma jakadu sun nuna damuwa kan abin da yake faruwa a Kenya, inda suka yi kira da a yi zaman tattaunawa domin shao kan matsalar.
BBC