Babban sakataren ma’aikatar jin kai da ci gaban jama’a, Dakta Sani Gwarzo, ne ya bayyana hakan a wani taron ba da katin cin gajiyar shirin inshorar lafiya ga waÉ—anda suka amfana a Abuja.
A cewarsa, matakin zai tabbatar da samar da ayyukan kula da lafiya cikin sauki ga masu buƙata ta musamman a fadin kasar.
Gwarzo ya yi wannan jawabi ne a lokacin da ya jagoranci jami'an ma'aikatar lafiya zuwa fadar sarkin Karo Majiji kuma shugaban masu buƙata ta musamman a Abuja.
Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya NAN ta ruwaito cewa hukumar kulla da masu buƙata ta musamman ta ƙasa (NCPWD) ce ta dauki nauyin yin rijistar.
An dauki matakin ne domin rage wahalhalun da mutane masu nakasa ke fuskanta wajen samun ayyukan kula da lafiya.
Ya ce gwamnati ta fara aiwatar da shirin ne a babban birnin tarayya kuma ana sa ran za a faÉ—aÉ—a shi zuwa jihohi 36 na Najeirya.