Mahukunta a filin tashin jiragen saman ne suka tabbatar wa da BBC afkuwar wannan lamari.
Tuni aka kaddamar da bincike don kama wadanda suka aikata wannan sata da kuma dawo da abin da suka sata.
Ba dai a san lokacin da aka sace fitilun a filin tashin jiragen sama na Murtala Muhammed da ke Legas ba.
Kodayake wasu kafafan yada labaran jihar sun ce ana zargin ma'aikatan filin jirgin saman da hannu a wannan sata.
A watan Nuwambar 2022 ne, aka sanya fitilun domin kara haske a wajen.
Saboda duhun wajen dole aka mayar da jiragen da ke zirga zirga a tsakanin jihohin Najeriya sauka da tashi a bangaren tashin jiragen kasashen waje.