A ranar 11 ga watan Yuli ne wani bidiyo da ya karaɗe shafukan sada zumunta, ya nuna wasu gungun mutum 11 na yi wa wata budurwa fyaɗe. Lamarin dai ya faru ne a garin Orama-etiti na jihar.
Cikin wata sanarwa da kakakin ƴan sandan jihar, Dsp Ikenga Tochukwu ya fitar, ta ce ƴan sandan jihar ta Anambra tare da haɗin-gwiwar ƴan sa-kai sun kama mutum shida cikin waɗanda ake zargi da aikata laifin.
Mutane shidan da aka kama sun amsa aikata laifin.
Ƴan sandan yayin wani samame, sun kama wasu mutum uku da zargin yi wa ƴar shekara 15 fyaɗe a Abagana.
Kwamishinan ƴan sandan jihar ya yaba wa jami'an tsaro da kuma ƴan sa-kai saboda ƙoƙari da suke yi na kakkaɓo ɓata-gari a cikin al'umma.
Ya sha alwashin daƙile batun fyaɗe da kuma cin zarafin mata da ake yi a jihar.
BBC