Mahukunta sun tabbatar da kashe mutum shida a yayin zanga-zangar.
A na su bangaren kungiyoyin kare hakkin dan adam sun ce mutum 12 aka kashe, tare da raunata wasu da dama.
'Yan sandan dai sun yi amfani da hayaki mai sa hawaye wajen tarwatsa mutane a Nairobi babban birnin kasar. An yi wa gwamman kananan yara magani a asibiti bayan sun shaki hayakin.
Tuni jagoran 'yan adawar kasar, Raila Odinga, ya bayar da umarnin dakatar da zanga-zangar gama-garin da aka shirya yi tun da farko don kaucewa karin tashin hankali, sai dai ya bukaci gwamnati ta janye shirin nata.