Babbar jam'iyyar adawa ta PDP a Najeriya ta ce ƙarin farashin man fetur da aka samu a ƙasar wanda ya kai naira 617 kan lita ɗaya rashin tausayi ne da ake nuna wa ƴan Najeriya.
A cikin wata sanarwa da ta fitar, mai ɗauke da sa hannun mai magana da yawun jam'iyyar na ƙasa Debo Ologunagba, jam'iyyar ta ce bai kamata a rinƙa sayar da litar man fetur a farashin da ya zarce naira 150 a Najeriya.
Sanarwar ta zargi gwamnatin Najeriya da gaza warware matsalar tattalin arziƙi da ƙasar ke fama da su, tare kuma da ƙoƙarin tsawwala wa jama'a.
A ranar Talata ne farashin man fetur a Najeriyar ya kai naira 617 a Abuja, da ma wasu sassan ƙasar.
Masana harkar man fetur dai sun ta'allaka batun a kan ƙarin farashin gangar ɗanyen mai a kasuwannin duniya da kuma faɗuwar darajar naira.
A ranar 29 ga watan Mayu ne shugaban Najeriya Bola Tinubu ya sanar da cire tallafin da gwamnatin ƙasar ke bayarwa a ɓangaren man fetur.
Lamarin da ya haifar da tashin farashin sufuri da kayan masarufi a faɗin ƙasar.