Wani mazaunin Abuja da ya bayyana sunansa da Abubukar kawai ya shaida wa BBC Hausa cewa a shafin sada zumunta ya ga batun ƙara farashin man fetur zuwa N617 da aka yi wayewar garin Talata a Najeriya.
Ya ce "Gaskiya ana kai talaka bango.
"Yau za ka tashi da wannan, in an jima ka saya. Ba ka san kuma gobe me za ka je ka tarar ba".
Ya ce kamata ya yi gwamnati ta duba halin da talakawan Najeriya ke ciki.
Ita ma wata mazauniyar Abuja ta ce abin takaici ne yadda aka wayi gari da ƙarin kuɗin man fetur ba zato ba tsammani.
"Babu wani bayani na cewa za a yi ƙarin (kuɗin man). Nawa ne albashin mutum da har za a yi ƙarin man fetur da tsada haka?" Ta tambaya.
Ta ce da tsakar rana ne kawai ta ga ana maganar ƙarin man fetur ɗin a shafin Tuwita.
"Kuma ga shi ina buƙatar na sha man a yau. Farashin da na gani ya kai N617, wannan abu ya wuce hankali. Ba mu gama sabawa da wancan ƙarin man fetur ba, sai ga wani. Ni, ban san yadda zan yi ba!"
An samu dogayen layukan ababen hawa a gidajen mai cikin wasu sassan Najeriya, bayan rahotannin ƙara farashin man fetur zuwa sama da N600 a kan lita ɗaya. Tun farko, an wayi gari ne da ƙarin kashi 22% a kan farashin N540 da ake sayar da man fetur ɗin a baya.
BBC ta fahimci cewa layukan ababen hawan sun faru a gidajen man da ba su kai ga ƙara farashinsu ba. Matakin na zuwa ne yayin da hukumar kayyade farashin man fetur ta kasar ta ce an samu raguwar man da ake sha a kasar daga lita miliyan 65 a kullum zuwa lita miliyan 35 a kullum.