Barista Mainasara Kogo babban lauya ne a Najeriya ya kuma ce majalisar dattawa majalisa ce da ta ƙunshi wakilai daga mazaɓu 109, inda kowacce jiha ke da 'yan majalisar dattawa uku, yayin da babban birnin tarayyar ƙasar Abuja ke da ɗan majalisar dattawa guda ɗaya.
A ɓangare guda kuma a majalisar wakilai ana amfani da girman ƙasa da yawan jama'ar wajen fitar da gundumomin 'yan majalisar, kamar yadda Barista Kogo ya bayyana.
''Wannan ne ma ya sa wani lokaci za ka ga an haɗa kananan hukumomi guda biyu, ko uku a matsayin gundumar dan majalisa ɗaya, wani lokaci kuma ƙaramar hukuma ɗaya ma za ta samu wakili guda, kasancewar tana da yawan jama'ar da ta kai samun matsayin gundumar ɗan majalisar wakilan'', in ji Lauya Kogo.
Sannan wani bambancin shi ne na shekarun 'yan majalisar, kamar yadda barista Kogo ya bayyana.
Ya ce ɗan majalisar dattawa kundin tsarin mulkin ƙasar ya ce sai wanda ya kai shekara 35 zuwa sama ne zai zama Sanata, amma a majalisar wakilai daga 25 ne zuwa sama.
Dangane da hurumin aiki kuwa Barista Kogo ya ce duka majalisun biyu aikinsu kusan irin É—aya ne, musamman ta fuskar yin dokoki da amincewa da kasafin kudi.
Babban abin da ya haÉ—a su shi ne yin dokoki, domin kuwa abu ba zai zama doka ba, dole sai duka majalisun biyu sun amince da shi, kamar yadda Barista Kogo ya bayyana.
Ya ƙara da cewa duk abin da majalisar wakilai za ta yi, to da dattawa ma za ta yi shi, amma kuma majalisar wakilai ba za ta iya duk aikin da majalisar dattawan ke yi ba.
''Alal misali majalisar dattawa ce kaɗai ke tantance ministoci da sauran naɗe-naɗen da shugaban kasar zai yi, sannan ita ke amincewa da naɗin manyan hafsoshin tsaro, da jakadun ƙasashen waje'', kamar yadda Lauyan ya bayyana
''Manyan hukumomin irin su EFCC da sauran hukomomi dole sai majalisar dattawa ta tantance, sannan ta amince da waɗanda shugaban ƙasar zai naɗa a matsayin shugabanninsu, amma ba majalisar wakilai ba'', in ji Barista Kogo.
BBC