Shugabannin sun tattauna kan al'amura da dama da suka shafi jihar, musamman tun bayan da Abba ya karɓi ragama a farkon watan Yuni, inda gwamnatinsa ke ci gaba jawo muhawara game da rushe-rushen da take yi.
Cikin abubuwan da suka tattauna har da batun sabon tallafin karatu da gwamnatin ta ɓullo da shi wanda kuma zai fara aiki a watan Satumba, a cewar gwamnan. Sarkin wanda ƙani ne ga Sarkin Kano Aminu Ado, ya gana da gwamnan bayan yayan nasa ya kai irin wannan ziyarar a ranar Juma'a yayin Hawan Nassarawa.